Bincike: 'Yan kasar Norway da dama na rungumar Addinin Musulunci

Malami a sashen nazarin Addinai a jami'ar Oslo da ke Kasar Norway Karin Vog ya bayyana cewar a 'yan shekarun nan al'umar Kasar na rungumar Addinin Musulunci.

Jaridar Verdens Gand da aka fi karantawa a kasar ta ce, daga shekarar 1990 zuwa yau 'yan kasar Norway na ta karba Addinin Musulunci.

Vog ya kuma ce, a baya mata na zabar hanyar yin aure da Musulunci ya koyar amma a yanzu suna bincike, neman Ilimi tare da rungumar Addinin.

An bayyana cewa, a shekarun 1990 Musulman Norway ba su fi 500 ba amma a yanzu sun haura dubu 3.

A wasu rahotanni da aka fitar a shelkarun baya Addinin Musulunci ne a kan gaba wajen samun karbuwa a nahiyar Turai.Labarai masu alaka