'Yar wasan dambe ta Turkiyya ta lashe kambin zinariya a gasar kasa da kasa

'Yar wasan dambe ta Turkiyya Busenaz Surmeneli ta lashe kambin zinariya a gasar share fagen kasashen Turai da ake yi a Paris Babban Birnin Faransa don halartar Gasar Wasannin Motsa Jiki ta Tokyo 2020.

1654606

Sanarwar da Tarayyar Wasannin Dambe ta Turkiyya ta fitar ta ce, Busenaz Surmenali ta samu nasara a gasar share fage ta mata masu nauyin kilogram 69 inda ta doke abokiyar karawarta 'yar kasar Jamus Nadine Apetz.

Busenaz ta isa wasan semi final don neman cancantar halartar gasar ta Tokyo 2020.

 Labarai masu alaka