Sifan ta kafa tarihi a gasar tsere ta mata ta kasa da kasa

'Yar kasar Holan kuma 'yar asalin kasar Itopiya Sifan Hassan ta kafa tarihi a gasar tsere ta mata ta duniya a waje mai nisan mita dubu 10.

1652868
Sifan ta kafa tarihi a gasar tsere ta mata ta kasa da kasa

'Yar kasar Holan kuma 'yar asalin kasar Itopiya Sifan Hassan ta kafa tarihi a gasar tsere ta mata ta duniya a waje mai nisan mita dubu 10.

Sifan Hassan ta samu nasara a gasar fa Tarayyar Wasannin Motsa Jiki ta Duniya ta shirya a garin Hengelo na kasar Holan bayan ta kammala zagayen a mintuna 29.06.82.

'Yar wasan mai shekaru 28 ta haura 'yar kasar Itopiya Almaz Ayana wadda ta yi zagayen a mintuna 29.17.45 a lokacin wasannin Olympics na Rio de Janero a shekarar 2016.

Sifan ta bayyana cewa, ta yi atisaye tukuru game da gasar Tokyo 2020.

Ta ce, "Wannan nasarar da na samu a yau a Hengelo abu ne da na dade ina fata. Ina farin ciki yadda masoyana na Holan suka ji dadin wannan nasara."Labarai masu alaka