Baturke ya lashe kambin zinariya da tagulla a gasar daga karafa ta Turai

Dan wasan daga karafa na Turkiyya Muhammed Furkan Ozbek ya lashe kambin zinariya 2 da na tagulla 1 a gasar daga karafa ta Turai.

1615469

A ranar ta 3 ta gasar da ake gudanarwa a Moscow Babban Birnin Rasha, dan wasan Turkiyya ya samu nasarar lashe kambi 3.

A bangaren maza da ke daga karfe mai nauyin kilogram 145, Ozbek ya samu kambin tagulla.

Haka zalika Ozbek ya lamshe kambin zinariya 2 bayan daga karafa masu nauyin kilogram 323 a bangarori 2 daban-daban.Labarai masu alaka