Messi ya sake kafa tarihi

Lionel Messi ya sake kafa tarihi wajen jefa kwallaye da kuma kuzarin buga wasanni.

1606377
Messi ya sake kafa tarihi

Lionel Messi ya sake kafa tarihi wajen jefa kwallaye da kuma kuzarin buga wasanni.

Dan wasan dan kasar Ajantina bayan buga wasa da Real Sociedad ya zarje Xavi inda ya zama dan wasan da ya fi kowanne saka riga a Barcelona.

Messi ya samu nasarar zama dan wasan da ya saka rigar Barcelona sau 768. Messi mai shekaru 34 da haihuwa ya dauki tsawon kakar wasanni 15 yana buga kwallo ba tare da sassautawa ba.

A wasanni 768 da ya buga a Barcelona, ya yi nasara sau 536, kunnen doki sau 140 da kuma rashin nasara 91.

Dan kwallon kafar na Ajantina ya jefa kwallaye 663 tare da lashe kofuna 34 wanda shi ne dan wasan da ya fi kowanne samun nasara a kungiyar.Labarai masu alaka