Gasar Zakarun Ingila: Chelsea ta doke New Castle da ci 2 da 0

A mako na 24 na gasar Zakarun Ingila (Premeir League), kungiyar Chelsea ta doke New Castle da ci 2 da 0.

1584440
Gasar Zakarun Ingila: Chelsea ta doke New Castle da ci 2 da 0

A mako na 24 na gasar Zakarun Ingila (Premeir League), kungiyar Chelsea ta doke New Castle da ci 2 da 0.

Chelsea da ta karbi bakuncin New Castle a filin wasa na Stamford Bridge, ta jefa kwallayenta 2 a zagayen farko na wasan.

Chelsea ta jefa kwallo ta farko a minti na 31 da fara wasa ta kafar dan wasanta Olivier Giroud, inda a minti na 39 kuma Timo Werner ya jefa kwallo ta 2.

Ba a jefa kwallo ba a zagaye na 2 wanda hakan ya sanya aka tashi wasan Chelsea na da kwallaye 2, New Castle kuma na nema.

Sakamakon nasarar da Chelsea ta yi, tana da maki 42 inda New Castle ke da maki 25 a gasar ta Zakarun Ingila (Premier League).Labarai masu alaka