'Yan wasan Bayern Munich 2 sun kamu da Corona

'Yan wasa 2 na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke Jamus Javi Martinez da Leon Goretzka sun kamu da cutar Corona (Covid-19).

1573895
'Yan wasan Bayern Munich 2 sun kamu da Corona

'Yan wasa 2 na kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich da ke Jamus Javi Martinez da Leon Goretzka sun kamu da cutar Corona (Covid-19).

Mai horar da 'yan wasan Bayern Munich Hansi Flick ya kira taron manema labarai kafin wasan mako na 19 na gasar Bundes Liga da kungiyar za ta buga da Hoffenheim.

Flick ya shaida cewar, bayan gwajin da aka yi wa Martinez da Goretzka an gano sun dauke a kwayar cutar Corona kuma sun killace kawunansu.

Ya kara da cewa, 'yan wasan ba za su saka riga ba a yanzu, kuma mai tsaron gida Alexander Nubel ma ba zai buga wasanni ba nan da makonni 3 zuwa 4 saboda raunin da ya samu a lokacin atisaye a ranar Alhamis din nan.Labarai masu alaka