An dauki matakin yaki da nuna wariya a gasar Premier ta Ingila

Mahukuntan gasar Premier ta Ingila sun dauki matakin samar da hanyar yin korafi da kai kara idan aka nuna wariya ga 'yan wasa, masu horar da su ko iyalansu a shafukan sada zumunta na yanar gizo.

1443640

Sanarwar da aka fitar daga ofishin shirya gasar ta Premier ta bayyana cewar za a iya kai kara ta shafukan sada zumunta idan aka ga nuna wariya, sannan kuma za a dauki matakin shari'a kan masu aikata hakan.

A shekarar da ta gabata ne 'yan wasan Manchester United Paul Pogba da Marcus Rashford suka gamu da nuna wariya wanda ya zama babban batun da aka dinga tattaunawa a kai.

Dan wasan Arsenal dan kasar Turkiyya Mesut Ozil ma yana yawan bayyana cewar ana aika masa da sakonnin nuna wariya a koyaushe.Labarai masu alaka