An sanar da lokacin fara gasar kwallon kwando ta Turkish Airlines ta 2020-2021

A watan Oktoban bana za a fara gasar kwallon kwando ta Turai ta kamfanin Turkish Airlines ta kakar wasanni ta 2020-2021.

1442865
An sanar da lokacin fara gasar kwallon kwando ta Turkish Airlines ta 2020-2021

A watan Oktoban bana za a fara gasar kwallon kwando ta Turai ta kamfanin Turkish Airlines ta kakar wasanni ta 2020-2021.

An bayyana cewar a ranar 1 ga watan Oktoban bana za a fara gasar ta kakar wasanni ta dubu 2020-2021 wadda aka dakatar a baya saboda annobar Corona (Covid-19).

A wasan farko da za a buga kıungiyoyin Anadolu Efes na Turkiyya da Zenit ta Rasha ne za su barje gumi.

 Labarai masu alaka