Corona: An dage lokacin gudanar gasar wasan ninkaya ta duniya

Sakamakon barazanar da annobar Corona (Covid-19) ke ci gaba da yi, an dage gasar ninkaya ta duniya (FINA) da aka shirya yi a garin Abu Dhabi Babban Birnin Hadaddiyar Daular Larabawa a watan Disamban bana.

1421440

Sanarwar da aka fitar daga Hukumar Shirya gasar ta ce an dage gasar da aka shirya yi a Abu Dhabi a watan Disamba zuwa bayan shekara daya bayan nazari game da lafiyar 'yan wasa.

Baya ga shekarar 2010, a karo na 2 kenan da birnin Abu Dhabi zai karbi bakuncin gasar wadda aka shirya yi a tsakanin 13 da 18 ga watan Disamban 2020.

Hukumar FINA ta ce an dage gasar wasan ninkaya da aka shirya yi a Japan a tsakanin 13 da 29 ga watan Mayun 2021 zuwa shekarar 2022.

 Labarai masu alaka