An sake dage lokacin dawowa buga wasannin kwallon kafa a Italiya

Tarayyar Kwallon Kafa ta Italiya ta (FIGC) ta dage lokacin dawo buga wasannin kwallon kafa da suka hada da na gasar Sirie A har sai nan da ranar 14 ga watan Yunin 2020.

1420001

FIGC ta fitar da sanarwar cewa sakamakon sassauta matakan yaki da Corona da Fadar Firaministan Italiya ta yi a ranar Litinin din nan, sun dauki matakin dakatar da dukkan harkokin wasannin kwallon kafa a kasar har sai nan da 14 ga watan Yunin 2020.

Rubutacciyar sanarwar da Tarayyar ta fitar ta ce, matukar ba wata sanarwa aka sake fitarwa daga wajensu a nan gaba ba, to ba za a sake buga wata gasa ba har sai nan da 14 ga watan Yuni.

A ranar 9 ga watan Maris ne aka fitar da doka daga Fadar Firaministan Italiya, inda aka dakatar da dukkan harkokin wasanni saboda annobar Corona da ta illata kasar sosai.Labarai masu alaka