Za a iya buga gasar kwallon Tennis a Faransa babu 'yan kallo

Shugaban Tarayyar Kwallon Tennis ta Faransa Bernard Giudecelli ya bayyana cewar akwai yiwuwar a buga gasar Kwallon tennis ta France Open da aka dage zuwa watan Satumba, ba tare da 'yan kallo.

1414941

Giudicelli ya zanta da jaridar Le Journal du Dimanche game da makomar gasar ta France Open (Roland Garros).

Ya ce za su dauki dukkan matakan da suka kamata, ko idan ta kama ma za a guda wannan gasa ba tare da barin 'yan kallo sun halarta ba.

A tsakanin 24 ga Mayu da 7 ga Yuni aka shirya yin gasar ta France Open, amma sakamakon annobar Corona (Covid-19) aka dage zuwa tsakanin 20 ga Satumba da 4 ga Oktoba.

An dage gasar kwararru ta Tennis zuwa 13 ga Yuli, an kuma soke gasar Wimbledon.Labarai masu alaka