Corona: An dage lokacin yin gasar kwallon dawaki ta St. George Golf 2020

Sakamakon annobar Corona (Covid-19) an dage lokacin gudanar da gasar kwallon dawaki ta St George Golf 2020.

1392743
Corona: An dage lokacin yin gasar kwallon dawaki ta St. George Golf 2020

Sakamakon annobar Corona (Covid-19) an dage lokacin gudanar da gasar kwallon dawaki ta St George Golf 2020.

An bayyana cewar an dage gudanar da gasar zuwa wani lokaci a nan gaba.

Sanarwar da ofishin shirya gasar ya fitar ta ce tun shekarar 1945 da aka fara yin gasar wannan ne karon farko da aka kasa gudanar da ita.

Sanarwar ta kara da cewar ya yi wuri idan masu ruwa da tsaki suka fadi yaushe za a gudanar da gasar ta St. George Golf 2020, za a dauki mataki ne duba da yadda al'amura suka kasance a duniya.

Daya daga cikin masu kula da shirya gasar Martin Slumbers ya ce sun yi kokarin ganin an gudanar da ita a wannan shekarar ta 2020 amma kuma ga dukkan alamu hakan ba zai yiwu ba.

 Labarai masu alaka