Ba za a sauya sunan gasar Olympics ta Tokyo 2020 ba

An dage lokacin gudanar da gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympics Tokyo 2020 zuwa shekarar 2021.

1384570
Ba za a sauya sunan gasar Olympics ta Tokyo 2020 ba

An dage lokacin gudanar da gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympics Tokyo 2020 zuwa shekarar 2021.

Shugaban Kwamitin Shirya gasar tare da Firaministan Japan Shinzo Abe ne suka sanar da an dage lokacin zuwa shekarar 2021.

Sunan gasar zai zauna a Tokyo 2020 kamar yadda aka tsara. Kwamitin Shirya gasar ya bayyana cewar wasannin na Olympics na Tokyo 2020 za su zauna da sunansu, amma za a gudanar da su a shekarar 2021.

Tun daga shekarar 1896 zuwa yau ake gudanar da gasar kuma har a lokacin yakin duniya na farko da na biyu an gudanar da ita, amma a karon farko saboda Corona (Covid-19) an dage lokacinta.

A wata wasika da Shugaban kwamitin Shirya gasar ta Olympics Tokyo 2020 Thomas Bach ya aikewa da wadanda za su halarta ya bayyana cewar "Rayuwar dan adam na gaba da komai har ma da wasannin Olympics. Hukumar Shirya gasar na son ku zama wani bangare na yaki da cutar Corona. Lafiyar kowa ita ce abu mafi fifiko a wajenmu. Muna cikin wata hanya da ba mu san ina za ta kai mu ba amma ina fatan za isar da mu ga wasannin Olympics."Labarai masu alaka