Za a dage gasar wasannin Olympics ta 2020 Tokyo

Mamban kwamitin shirya gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympics ta 2020 Tokyo Dick Pound ya bayyana cewar sakamakon annobar Corona (Covid-19) an dage lokacin gudanar da gasar.

1384095
Za a dage gasar wasannin Olympics ta 2020 Tokyo

Mamban kwamitin shirya gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympics ta 2020 Tokyo Dick Pound ya bayyana cewar sakamakon annobar Corona (Covid-19) an dage lokacin gudanar da gasar.

Pound, da ya zanta da 'yan jaridun Amurka ya bayyana cewar akwai yiwuwar saboda annobar Corona (Covid-19) sai a shekarar 2021 za a buga wasannin gasar ta Olympics 2020 Tokyo, ma'ana an ma yanke hukuncin dage lokacin.

Ya ce, bisa bayanan da yake da su ba a ranar 24 ga watan Yuli za a fara gasar ba, kuma suna yin duk mai yiwuwa wajen ganin sun warware matsalar.

An shirya gudanar da gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympics a tsakanin 24 ga Yuli da 9 ga Satumban 2020 a Tokyo Babban Birnin Japan.

A baya dai shugaban Kwamitin Shirya Wasannin Olympics na Kasa da Kasa Thomas Bach ya bayyana cewar ana ci gaba da shirye-shiryen gasar Olympics ta Tokyo 2020 kamar yadda aka tsara. 

Bach ya ce, shirya harkokin gasar ba kamar sake buga wasan kwallon kafa ba ne, yana bukatar nutsuwa da kula sosai.

Ya kuma ce idan har aka soke wasan to za a karya zukatan 'yan wasa kusan dubu 11, kuma an tanadi abubuwan da ya kamata game da batun soke gasar da aka shirya yin ta a bazarar 2020.

A gefe guda tawagar Sabiya da Kuroshiya sun bayyana cewar sun dauki matakin hakura da halartar gasar ta bana.

Mai wasan takobi dan kasar Jamus Max Hartung ya ce idan har aka yanke hukuncin gudanar da gasar to zai kaurace mata baki daya.

Hartung ya ce Japan ba ta da hujjar cewa dole sai an yi gasar, kuma akwai bukatar kowa ya taka rawa wajen hana cutar yaduwa.

Haka zalika Hukumomin wasannin ninkaya da tsalle-tsalle na kasashen Amurka, Faransa, Ingila da Barazil sun bukaci a dage lokacin gudanar da gasar.

Amma gwamnatin Japan da zuwa yanzu ta kashe kimanin dala biliyan 12 saboda gasar ba ta nuna alamun tana so a dage lokacin yin ta.

Bayanan da aka suka fita daga kwamitin shirya gasar na cewar akwai hanyoyi 3 game da ita.

Na farko a dage ta zuwa bayan shekaru 2, na 2 kuma a fara a watan satumba sai na 3 shi ne a yi babu 'yan kallo.Labarai masu alaka