An samu shugabannin Galatasaray dauke da cutar Corona

Kungiyar Kwallon Kafa ta Galatasaray dake Turkiyya ta girgiza game da kamuwa da cutar Corona (Covid-19) da wasu shugabanninta suka yi.

1383866
An samu shugabannin Galatasaray dauke da cutar Corona

Kungiyar Kwallon Kafa ta Galatasaray dake Turkiyya ta girgiza game da kamuwa da cutar Corona (Covid-19) da wasu shugabanninta suka yi.

Bayan samun Shugaba na 2 na Galatasaray Abdurrahman Albayrak dauke da cutar, an samu mai horar da 'yan wasanta Fatih Terim ma dauke da ita.

Mai horar da 'yan wasan ya fitar da wannan labari mara dadi ta shafinsa na Twitter.

A sanarwar da Terim ya fitar ya ce "Bayan gwajin da aka yi min an same ni dauke da cutar Corona. Ina asibiti a hannun amintattu. Kar ku damu. Za mu gana da juna nan da wani dan lokaci."

Bayan gwajin da aka yi ba a samu matamakan Terim, Umit Davala da Hasan Shash dauke da cutar ba.Labarai masu alaka