Corona: An dakatar da gasar NBA

Sakamakon barazanar da cutar Corona (Covid-19) ke ci gaba da yi an dakatar da dukkanin wasannin gasar kwallon kwando ta Amurka (NBA).

1376941
Corona: An dakatar da gasar NBA

Sakamakon barazanar da cutar Corona (Covid-19) ke ci gaba da yi an dakatar da dukkanin wasannin gasar kwallon kwando ta Amurka (NBA).

Bayan samun daya daga cikin 'yan wasan Utah Jazz dauke da cutar ta Coron ne aka dakatar da dukkan wasannin da ake yi.

Ba a bayyana sunan dan wasan ba, sakamakon yadda aka sanar da ya kamu da Corona kafin wasan da Utah Jazz da Oklahoma City Thunder za su buga, ya sanya an dakatar da buga wasan.

Sanarwar da aka fitar ta ce a lokacinda aka zo buga wasan, wanda aka samu dauke da cutar ta Corona ba ya filin wasa.Labarai masu alaka