Corona ta fara shafar harkokin wasanni a duniya

Shafin yanar gizo na Hukumar Kula da Kwallaon kafa ta Japan ya sanar da cewar sakamakon yaduwar cutar Corona an dage wasannin da aka shirya buga wa na gasar Zakaru ta Kasar a ranar Alhamis din nan.

Sanarwar ta ce an kuma dage lokacin buga dukw asu wasanni da aka shirya yin su nan da ranar 15 ga watan Maris.

A baya an bayar da gargadi game da gasar wasannin tsalle-tsalle ta Tokyo-2020 da za a gudanar a tsakanin 24 ga Yuli da 9 ga Agustan bana.

Har yanzu ana ci gaba da zuba ido kan ko za a soke gudanar da gasar.

Hukumar Kula da Wasannin Kwallon Tennis ta Duniya ta sanar da ge lokacin da za a gudanar da gasar kasa da kasa a garin Busan na Koriya ta Kudu.

Haka zalika an dage lokacin gudanar da gasar kwallon kafa ta Zakarun Koriya ta Kudu da aka shirya fara gudanarwa a wannan makon.Labarai masu alaka