Ana ci gaba da buga wasanni a gasar Zakarun Turkiyya

A mako na 23 na gasar kwallon kafa ta Zakarun Turkiyya, kungiyar Medipol Basaksehir (Bashakshehir) ta buga wasan farko da Caykur (Chaikur) Rizespor.

1365717

A wasan da aka buga a filin wasa na Caykur Didi, Basaksehir ta yi nasara da ci 2 da 1.

A minti na 41 da fara wasa Basaksehir ta jefa kwallo ta farko ta hanun Edin Visca inda Rizespor kuma ta farke kwallon a minti na 60 ta hannun dan wasanta Aminu Umar.

Dan wasan Basaksehir Martin Skrtel da ya shiga wasan a minti na 91 ya kawo wa kungiyarsa babbar nasara.

Wannan nasara ta ba wa Basaksehir damar zama jagora da maki 46.

Rizespor kuma tana da maki 24.Labarai masu alaka