Za a gudanar da wasan kwallon dusar kankara ta bana a Turkiyya

A tsaunin Erciyes na Turkiyya a tsakanin 12 d 15 ga watan Maris din 2020 za a gudanar da wasan kwallon Volleyball ta kasa da kasa.

Za a gudanar da wasan kwallon dusar kankara ta bana a Turkiyya

A tsaunin Erciyes na Turkiyya a tsakanin 12 d 15 ga watan Maris din 2020 za a gudanar da wasan kwallon Volleyball ta kasa da kasa.

A wannan shekarar za a gudanar da gasar a karo na 2 wadda Tarayyar kwallon Volleyball ta duniya take shiryawa.

Za a gudanar da zagaye na farko na gasar a Tsaunin Erciyes na Turkiyya a tsakanin 12 da 15 ga watan Maris. Za kuma a gudanar da zagaye na biyu a kasar Ajantina a tsakanin 20 da 23 ga watan Agusta.

Tarayyar Kwallon Volleyball ta Turkiyya ta samu nasarar halartar gasar da ake shiryawa a nahiyar Turai har sau 7.

A shekarar 2018 Turkiyya ta lashe kambin tagulla a bangaren mata na gasar da aka buga a Ostireliya.Labarai masu alaka