Munin yanayi ya sanya dage wasu wasanni a Turai

Sakamakon munanar yanayi an dage buga wasannin kwallon kafa a karshen makon da ya gabata a kasashen Jamus, Holan da Beljiyom.

Munin yanayi ya sanya dage wasu wasanni a Turai

Sakamakon munanar yanayi an dage buga wasannin kwallon kafa a karshen makon da ya gabata a kasashen Jamus, Holan da Beljiyom.

A gasar Bundesliga ta Jamus an dage wasan da Borussia Monchengladbach za ta buga da Cologn.

A Holan kuma munin yanayi ya sanya dage wasannin gasar zakaru ta kasar.

A Beljiyom ma lamarin haka yake inda aka kasa buga wasannin gasar zakaru na farko da na 2 wanda aka mayar da su ranakun Laraba da Alhams.Labarai masu alaka