An kasa yin nasara a kan Liverpool a wasanni 40 da ta buga a jere

A mako na 24 na gasar Premier ta kasar Ingila kungiyar Liverpool ta doke Wolverhampton Wanderers da ci 2 da 1.

An kasa yin nasara a kan Liverpool a wasanni 40 da ta buga a jere

A mako na 24 na gasar Premier ta kasar Ingila kungiyar Liverpool ta doke Wolverhampton Wanderers da ci 2 da 1.

A wasan da aka buga a filin wasa na Molineux Ground, Liverpool da ta kafa tarihi ta je gidan Wolverhampton Wanderers.

Liverpool ta fara wasan cikin nasara inda a minti na 8 da take leda ta jefa kwallo 1 ta hannun Jordan Henderson.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci dan wasan Wolverhampton Wanderers Raul Jimenez ya farke kwallon inda wasan ya koma 1 da 1.

A minti na 84 kuma dan wasan Liverpool Roberto Firmino ya je kwallo ta 2.

A yanzu Liverpool ta buga wasanni har sau 40 a jere inda aka kasa samun nasara a kanta.

Kungiyar na da maki 67 a gasar Premier ta bana.Labarai masu alaka