Tsananin sanyi na kashe mutane a Afganistan

Sakamakon zubar dusar kankara da tsanantar sanyi a jihar Logar din Afganistan mutane 5 dake wani sansanin masu nrman mafaka sun rasa rayukansu.

Tsananin sanyi na kashe mutane a Afganistan

Sakamakon zubar dusar kankara da tsanantar sanyi a jihar Logar din Afganistan mutane 5 dake wani sansanin masu nrman mafaka sun rasa rayukansu.

Kakakin Fadar Gwamnan Logar, Didar Ahmad Lavang ya ce, tsawon kwanaki ana ta ruwan dusar kankara a jihar wanda hakan ya janyo sanyi ya yi tsanani.

Lavang ya kara da cewar sakamakon tsanantar sanyin mutane 5 dake zaune a sansanin masu neman mafaka na tsakiyar Logar sun mutu, lamarin ya munana a yankin.

Ya ce sakamakon sanyin an dakatar da zirga-zirgar ababan hawa a gundumomi da dama na Logar.Labarai masu alaka