Real Madrid ta isa wasan karshe a gasar Super Cup ta Spaniya

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Spaniya real Madrid ta isa wasan karshe a gasar Super Cup bayan ta doke Valencia da ci 3 da nema a wasan da suka buga a Saudiyya.

Real Madrid ta isa wasan karshe a gasar Super Cup ta Spaniya
Jeddah, Saudi Arabia.JPG
Valencia  Real Madrid - King Abdullah Sports City.JPG
Valencia v Real Madrid.JPG
Valencia v Real Madrid modric.JPG

Kungiyar kwallon kafa ta kasar Spaniya real Madrid ta isa wasan karshe a gasar Super Cup bayan ta doke Valencia da ci 3 da nema a wasan da suka buga a Saudiyya.

Valencia da Real Madrid ne suka buga wasan na Semi Final a kasar waje a karon da manufar kara yawan kudaden shigar da ake samu a gasar La Liga.

A wasan da aka buga a filin wasannin na Sarki Abdullah dake Jeddah Real Madrid ta jefa kwallaye 3 ta hannun 'yan wasanta Toni Kroos a minti na 15, Isko a minti na 39 da Luka Modric a minti na 65 da fara wasan.

Valencia ta jefa kwallonta 1 ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida wanda Danie Parejo ya buga.

Real Madrid ba ta je Saudiyya da Karim Benzema da Gareth Bale ba sakamakon rashin lafiya.

 Labarai masu alaka