Shahararren mawakin Turkiyya ya yi wasa a Jamus

Shahararren mawakin duniya dan kasar Turkiyya Tarkan ya barje gumi a garin Koln dake kasar Jamus

1327455
Shahararren mawakin Turkiyya ya yi wasa a  Jamus

Shahararren mawakin duniya dan kasar Turkiyya Tarkan ya barje gumi a garin Koln dake kasar Jamus.

A yayinda yake rangadi a Nahiyar Turai ya yada zango garin Koln inda ya cashe a dakin wasannin Lanxess Arena inda masoyarsa kusan dubu takwas suka saurare shi.

Kanfanin da ta shirya wasan ta bayyana cewa an sayar da dukkanin tikitin da aka fitar.

Jarumin ya kwashe awanni biyu yana rera waka lamarin da farantawa masu sauraro rai.

A dakin wasanni da ya cika makil da Turkawa da Jamusawa Tarkan ya yi nasarar burge kowa domin an tafa masa.

 Labarai masu alaka