Fonseca: Dole Under ya yi wa kansa garambawul

Kocin Kungiyar Kwallon Kafar Roma Paulo Fonseca ya bayyana cewa dole Cengiz Under ya yi wa kansa garambawul yayinda ya ce hazakar da ya nuna a wasan da ya buga na karshe bata isa ba.

Kocin ya ce wasan da za su buga da Inter Milan a gobe tamkar dama ce ta nuna kwarewarsu.

Kamar haka ne dai kocin ya shirya taron 'yan jarida kafin su tafi gidan Inter a gobe inda za su taka leda a mako na 15 domin lashe Gasar Serie A. 

A lokacin ne dai aka tambayi kocin da cewa ko ya ji dadin wasan da Under ya buga bayan dawowarsa daga hutun rashin lafiya inda ya ce, "dole Under ya yi wa kansa garambawul". 

Tag: Fonseca , Under

Labarai masu alaka