Ibrahimovic zai koma Italiya

Zlatan Ibrahimovic ya bayyana cewa zai koma Italiya bayan ya kamalla yarjejeniyarsa da kungiyar kwallon kafar Amurka ta Los Angeles Galaxy.

Ibrahimovic zai koma Italiya

Zlatan Ibrahimovic ya bayyana cewa zai koma Italiya bayan ya kamalla yarjejeniyarsa da kungiyar kwallon kafar Amurka ta Los Angeles Galaxy.

Ya yi jawabin ne a wani taron 'yan jarida inda wani dan jaridan Italiya ya jajirce wajen tambayar inda Ibrahimovic zai koma bayan Amurka. 

A nan ne dai Ibrahimovic ya ce, "za ku iya gani na a Italiya cikin kankanin lokaci".

Kamar haka ne dai dan wasan ya tabbatar da labaran da suka yadu kan cewa zai koma Milan ko kuma Napoli. 

Ibrahimovic ya kasance yana taka leda a Inter Milan inda ya daga kofin sau 4 a Gasar Serie A. 

 Labarai masu alaka