City ta bawa Burney kashi da ci 4 da 1

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta ba wa Burnley ka shi da ci 4 da 1 a wasan Firimiya da aka buga a gidan Burnley inda da yin haka City ta kammala mako na 15 da nasara.

Gabriel Jesus ne ya ci wa City kwallo biyu a minti na 24 da minti na 50 inda Rodri ya zura daya a minti na 68 sai kuma Riyad Mahrez ya cika ta hudu a minti na 87. 

Burnley ba ta samu dama ba sai har a minti na 89 inda Robbie Bradly ya ci mata kwallo daya a minti na 89. 

Bayan wannan wasan ne dai makin Manchester City ya kai 32 yayinda Burnley ta tsaya a maki na 18. Labarai masu alaka