Messe ya lashe Ballon d'Or

An kammala Babban Taron Kyautar Yabo da Mujallar Kwallon Kafa ta kasar Faransa ta shirya inda aka ba wa Messi kyautar gwarzon kwallon kafa na shekarar 2019 wato Ballon d'Or.

Messe ya lashe Ballon d'Or

An kammala Babban Taron Kyautar Yabo da Mujallar Kwallon Kafa ta kasar Faransa ta shirya inda aka ba wa Messi kyautar gwarzon kwallon kafa na shekarar 2019 wato Ballon d'Or.

Dan wasan mai shekaru 32 ya taba lashe kyautar sau 5 a shekarar 2009, 2010, 2011, 2012 da 2015 inda a wannan karon ma ya lashe ta 2019 inda da yin haka ya fi dukkan wani dan wasa samun kyautar. 

Ronaldo ne ya biyo bayansa to sai dai wannan karon bai halarcin taron bikin bada kyautar ba. 

Ila yanzu dai Messi ya zura kwallaye 46 a shekarar 2019 yayinda yake sake da rigar Barcelona da kuma ta Ajantina. 

A gefe guda 'yar wasan kungiyar kwallon kafar Amurka, Megan Rapinoe ce ta lashe kyautar Ballon d'Or ta mata a wannan shekarar. 

 Labarai masu alaka