An bude katabaren sabon filin kwallon kasar Japan

An kammala filin kwallon kasar Japan dake Tokyo wanda zai kasance babban filin da zai saukar da baki a gasar Olympic Games na shekarar bara

An bude katabaren sabon filin kwallon kasar Japan

An kammala filin kwallon kasar Japan dake Tokyo wanda zai kasance babban filin da zai saukar da baki a gasar Olympic Games na shekarar bara.

A ranar asabar ne aka mika filin jirgin ga Hukumar Wasannin kasar Japan wacce zata ci gaba da kula na al’umaransa.

A cikin watan jiya ne dai aka kammala gina filin wasan wanda zai iya daukar mutane dubu 60 amma a ranar Asabar din anan ne aka bude filin domin fara shirya ayyuka akallan watanni takwas gabanin fara gasar ta 2020.

Za’a dai fara wasa a ciki ne a ranar 21 ga watan Disamba da wasan Emperor's Cup wanda zai kasance wasa na farko a filin.

Wani jami’i shirya wasannin Tokyo 2020 Games mai suna Toshiro Muto ya bayyana cewar muna masu matiukar farin cikin kammala wannan katabaren aikin gina filin wasannin wanda zai zama cibiyar Tokyo 2020 games. Ya kara da cewa wannan alama ce dake nuna cewa mun shirya kuma muna kusa da Tokyo 2020 Games.

Muna shirye ga tarbon ‘yan wasa daga sassa daban daban na duniya wadanda zasu taka leda a sabon filin wasan ta kasar Japan. Tabbas duniya zata kayata daga wannan katabaren sabon filin wasanni a gasar Tokyo 2020.Labarai masu alaka