Unai ya yi bankwana da Arsenal

Mai horar da 'yan wasan kwallon kafar kngiyar Arsenal Unai Emery ya sanar da kawo karshen aiki da kungiyar.

Unai ya yi bankwana da Arsenal

Mai horar da 'yan wasan kwallon kafar kngiyar Arsenal Unai Emery ya sanar da kawo karshen aiki da kungiyar.

Sanarwar da aka fitar a shafin yanar gizon kungiyar ta ce "Mai horar da 'yan wasanmu Unai Emery tare da sauran masu taimaka masa sun kawo karshen aikinsu."

Kochin dan kasar Spaniya ya jagoranci Arsenal ta buga wasanni 78 kuma ya samu maki 1,85 inda ya yi rashin nasara a wasanni 7 na karshe da suka buga.

Arsenal ta sanar da sunan Freddie Ljungberg a matsayin mai horar da 'yan wasanta na wucin gadi.


Tag: Kochi , Unai , Arsenal

Labarai masu alaka