Anadolu Efes ta lallasa Bayern Munich da ci 104-74

Kungiyar kwallon kwandon kasar Turkiyya da Kanfanin Jirgin Saman Turkiyya ke daukar nauyi mai suna Anadolu Efes ta lallasa abokiyar hamayyarta ta Bayern Munich da ci 104-74 a gasar Nahiyar Turai

Anadolu Efes ta lallasa Bayern Munich da ci 104-74

Kungiyar kwallon kwandon kasar Turkiyya da Kanfanin Jirgin Saman Turkiyya ke daukar nauyi mai suna Anadolu Efes ta lallasa abokiyar hamayyarta ta Bayern Munich da ci 104-74 a gasar Nahiyar Turai.

Dan wasan Kungiyar Anadolu Efes Shane Larkin ya samu maki 49 a gasar wanda ba'a taba samu ba a tarihin gasar ta Nahiyar Turai.

Anadolu Efes ta yi nasarar lashe wasanni biyar cikin tara jere ga juna.

Ta kuma yi nasarar lallasa Bayern Munich har sau bakwai.

 Labarai masu alaka