An ci tarar Sergen Yalcın

Hukumar Kwallon Kafar Turkiyya ta haramta wa Kocin Malatyaspor Sergen Yalcın halartar wasanni 4 masu zuwa.

An ci tarar Sergen Yalcın

Hukumar Kwallon Kafar Turkiyya ta haramta wa Kocin Malatyaspor Sergen Yalcın halartar wasanni 4 masu zuwa.

Bayanin ya zo bayan an kammala wasan Kasimpasa da Malatyaspor inda aka daga wa Sergen Yalcın janka kati kan cewa halayyarsa ta saba wa ka'adiar hukumar kwallon kafa. 

Kamar haka ne dai aka ci tararsa Lira dubu 26 yayinda aka haramta masa halartar wasanni 4 masu zuwa.

Haka zalika an ci tarar dan wasan Kasimpasa mai suna Veysel Sarı inda aka hana shi buga wasanni 3 masu zuwa sannan aka tilasta masa biyan Lira dubu 26. 

Hakan ya faru ne dai bayan wata rigima da ya tada bayan an kammala wasan.

Hukumar Kwallon Kafar Turkiyya ta ci tarar 'yan wasa a wannan kakar kamar yanda ba a taba gani a da ba.Labarai masu alaka