Madrid ta ba wa Galatasaray kunya

Real Madrid ta ba wa Galatasaray kashi da ci 6 da 0 a Gasar Cin Kofin Zakarun Turai inda hakan ya yi sanadin fitar Galatasaray daga gasar duk da cewa ana mako na 4 a gasar.

Kamar haka ne dai Galatasaray ta yi asarar wasannin ta 16 masu zuwa. 

Madrid ta zura kwallaye 4 a ragar Galatasaray kafin a tafi hutun rabin lokaci inda aka ci kwallaye 3 na farko a mintina 14 na farko. 

Wasan an kamallashi ne a minti na 92 da ci 6 da 0 inda makin Real Madrid ya koma 7 yayinda na Galataray take da maki 1 a tebirin gasar. 

Dan wasan Madrid Rodrygo mai shekaru 18 ne yafi jan hankalin kowa yayinda ya zura kwalleye 3 shi kadai. 

 Labarai masu alaka