Joe Tsai ya sayi kaso a NBA

Daya daga cikin manajojin kanfanin Alibaba Joe Tsai ya sayi kaso 51 cikin dari na kulob din kwallon kwando mai suna Broolyn Nets wanda babban kulob ne a NBA.

1272934
Joe Tsai ya sayi kaso a NBA

Daya daga cikin manajojin kanfanin Alibaba Joe Tsai ya sayi kaso 51 cikin dari na kulob din kwallon kwando mai suna Broolyn Nets wanda babban kulob ne a NBA. 

A ranar Laraba shugabannin kulob din suka amince da sayar da kason. 

Daya daga cikin shugabanin Adam Silver ya wallafa jawabi da cewa, 

"Muna farincikin shelanta cewa Joe Tsai ya zama daya daga cikin manyan shugabannin Brooklyn Nets".

A lokaci guda Tsai na rike da shararren kanfanin Intanet mai suna Alibaba.

Tsai ya saya kaso 51 cikin dari na kulob din ne daga hannun dan Rasha Mikhail Dmitrievitch Prokhorov. Labarai masu alaka