Chelsea ta sabunta kwantiragi da N'Golo Kante

Kungiyar kwallon kafa ta Ingila Chelsea ta sake sabunta kwantiragi da dan wasan Faransa N'Golo Kante zuwa shekarar 2023 wadda a ka'ida za ta kare a shekarar 2021.

Kante ya ce, ya yi farin cikin ci gaba da kasancewa da kungiyar ta Ingila inda ya fadi cewar "Na taka leda a kakar wasanni 2 a nan kasar. Na samu nasarorin da ban zata ba. Ina son wannan kungiyar. Kuma na gamsu da yadda na ke zaune a nan."

A shekarar 2016 ne N'Golo Kante ya tafi Chelsea inda ya samu nasarar lashe League babba da karami.

A yayin gasar cin kofin duniya da aka buga a bana a Rasha, N'Golo Kante ya taka rawa sosai a kungiyar Faransa da ta yi nasara.

Ya taba zaba Zakaran Premeir League ta Ingila.Labarai masu alaka