An gudanar da gagarumin bukin rawa a Astana babban birnin Kazagystan

An bayyana gudanar da taron rawa na kasa da kasa a Astana babban birnin Kazagystan da aka yiwa taken (The Spirit of Dance) Festival.

Bukin da ma'aikatan al'adun Kazagystan din ta shirya a dakin taron kasar ya samu halartar 'yan rawa daga kasashen Kazagystan, Kırgyzstan, Azerbaijan, Uzbekistan, Rasha, Jojiya, Letoniya, Indiya, Amurka, Island da Kanada.

Mawaka sun rera wakoki da yarukan kasarsu inda 'yan rawa suka shakata a dakin taron.

An dai shirya wannan bukin ne domin yada al'adu da bunkasa waka da rawar gargajiyyar kasashen.

 Labarai masu alaka