Wasanni: Tolga ya koma Fenerbahce

An bayyana cewar dan kwallon Galatasaray mai suna Tolga Cigerci wande yake midfielder ya sauya sheka zuwa Fenerbahce.

Wasanni: Tolga ya koma Fenerbahce

An bayyana cewar dan kwallon Galatasaray mai suna Tolga Cigerci wande yake midfielder ya sauya sheka zuwa Fenerbahce.

Fenerbahce ta yada a shafinta na yanar gizo da cewa ta rataba hannu da dan shekara 26 mai suna Cigerci.

A ranar Laraba ne dai kungiyar Galatasaray da Tolga suka kawo karshen yarjejeniyar dake tsakaninsu.

A shekarar  2016-2017 ne Galatasaray ta rataba hannu da Cigerci har na shekaru uku a lokacin da yake bugawa wata kungiyar kwallon kafa a Jamus mai suna Hertha Berlin.

A ranar Alhamis kuma Fenerbahce ta karbi dan wasa mai tsaron gida daga Bursaspor mai suna Harun Tekin.Labarai masu alaka