Cinikin sayen Ronaldo ya haifar da babban rikici a Italiya

Ma'aikatan kamfanin samar da motoci na Fiat da suka dade suna jiran karin albashi sun shirya tafiya yajin aiki daga ranar 15 ga Yuli sakamakon yadda kkamfanin zai yi amfani da kudadensa wajen sayen dan wasan kwallon kafa Christiano Ronaldo.

Cinikin sayen Ronaldo ya haifar da babban rikici a Italiya

Ma'aikatan kamfanin samar da motoci na FIAT da suka dade suna jiran karin albashi sun shirya tafiya yajin aiki daga ranar 15 ga Yuli sakamakon yadda kamfanin zai yi amfani da kudadensa wajen sayen dan wasan kwallon kafa Christiano Ronaldo.

Kungiyar kwaago ta Italiya (USB) ta yi kira ga ma'aikatan kamfanin na Fiat da ke garin Melfi da su tafi yaji aiki.

Sanarwar da USB ta fitar ta ce, a lokacin da ma'aikatan Rukunin kamfanunnunak FIAT da CNH suka dauki tsawon lokaci suna sadaukar da kansu wajen habaka tatalin arzikin kamfanunnukan, to ba za a amince da sayen dan wasan da daruruwan miliyoyin Yuro ba da kamfanunnukan za su yi.

Sanarwar ta USB ta kara da cewa, sakamakon haka daga karfe 10 na daren ranar 15 ga Yuli zuwa karfe 6 na Asubahin 17 ga watan suna kira da ma'aikatan FIAT da su tafi yajin aikin gargadi. 

Kungiyar ta dauki wannan mataki ne bayan da Kungiyar Juventus mallakin mai kamfanin CNH Andrea Agnelli ta bayyana za ta sayi Ronaldo kan kudi har Yuro miliyan 120.

An bayyana cewa, ma kowacce shekara za a ba wa dan wasan Yuro miliyan 30 wato an saye shi na tsawon shekaru 4 kenan.Labarai masu alaka