FIFA 2018: Faransa da Kuroshiya ne za su fafata a wasan karshe

A wasan Semi Final da aka buga a gasar cin kofin duniya da ake ci gaba da yi a Rasha, Kuroshiya ta doke Ingila da ci 2 da 1.

FIFA 2018: Faransa da Kuroshiya ne za su fafata a wasan karshe

A wasan Semi Final da aka buga a gasar cin kofin duniya da ake ci gaba da yi a Rasha, Kuroshiya ta doke Ingila da ci 2 da 1.

Dan wasan Ingila Kieran Trippier  ne ya fara jefa kwallo a ragar Kuroshiya a mintina 5 da fara wasa.

Bayan an dawo hutun eabin lokaci 'yan wasan Kuroshiya Ivan Perisic da Mario Mandzukic suka jefa kwallaye daya-daya a ragar Ingila a mintuna na 68 da 109.

Sakamakon haka Kuroshiya za su kece raini da Faransa a wasan karshe a ranar 15 ga watan Yuli.

 Labarai masu alaka