Wani mai kaunar Ronaldo ya yi tafiyar kilomita dubu 5,100 a kan keke don ganin dan wasan

Dan Kasar Portugal Mai Kaunar Zakaran Dan Wasan kasar Christiano Ronaldo mai suna Helder Batista ya yi tukin keke na kilomita dubu 5,100 don ganin gwarzon nasa.

batista bisiklet.jpg

Dan Kasar Portugal Mai Kaunar Zakaran Dan Wasan kasar Christiano Ronaldo mai suna Helder Batista ya yi tukin keke na kilomita dubu 5,100 don ganin gwarzon nasa.

An sake samun mai goyon bayan Portugal da ya bi ta kasashen Turai da dama ya shiga Rasha.

Mai tseren keken dan kasar Portugal Helder Batista a ranar 6 ga watan Mayu ya hau keke a garin Alenquer na arewacin Lizbon inda ya yi tukin kilomita dubu 5,100 tare da isa Birnin Moscow na Rasha.

Ya yi tafiyar kusan kwanaki 45 inda ya ce, babbar matsalar da ya fuskanta ita ce yadda sauraye suka cicciji cinyoyinsa.Labarai masu alaka