Senegal ta ragargaji Poland

Kungiyar kwallon kafa ta Senegal Lions de la Teranga, wato "Zakunan Teranga" ta fitar da Afirka kunya,saboda ta zama tawaga daya tak wacce a yanzu haka ta shiga gasar cin kofin duniya da kafar dama ta hanyar ragargazar Poland  da ci 2 da 1.

Ta faru ta kare! Senegal ta lallasa Poland ci 2 da 1,a wasanta ta farko a gasar cin kofin duniya ta Rasha shekarar 2018.

Rashin dabara da kyaukyawan tsarin wasa na 'yan kasar Poland sun  tirsasa su durkusawa gaban takwarorinsu na Senegal,wadanda suka fi su kuzari da nutsuwa.

A minti na 38,dan wasan Poland Cionek ya maka kwallo a ragar gida,a yayin a dakika na 60 kuma, dan Senegal Mbaye Niang ya saka kwallo a ragar Poland bayan da 'yan wannan kasar Szczesny da Krychowiak  suka tafka babban kuskure.

A minti na 86 dan wasan Poland Grzegorz Krychowiak ya saka kwallo a ragar Senegal.

Wannan murnar ta wucin ga  ta sa Poland  harzuka da kara kyami don yin kunnen doki da Sanagal,amma har aka kamalla wasa ba cim ma burinta ba.

Abinda yasa kungiyar "Zakunan Teranga" ta kasance a jerin kungiyoyin wasan kwallon kafa na duniya ta rukuni H,wadanda suka ciri tuta a tashin farko a gasar bana.

A yanzu haka japan ce a sahun gaba a wannan rukunin na H.

 Labarai masu alaka