‘Yan wasan Afirka 5 sun sake yin layar zana a wajen wasannin tsalle-tsalle a Ingila

An sake sanar da batan wasu ‘yan wasan tsalle-tsalle na Afirka da suke halartar Gasar Wasannin Kungiyar Kasashe Rainon Ingila, inda adadin wadanda suka bace ya zuwa yanzu ya kama 'yan wasa 13.

‘Yan wasan Afirka 5 sun sake yin layar zana a wajen wasannin tsalle-tsalle a Ingila

An sake sanar da batan wasu ‘yan wasan tsalle-tsalle na Afirka da suke halartar Gasar Wasannin Kungiyar Kasashe Rainon Ingila, inda adadin wadanda suka bace ya zuwa yanzu ya kama mutane 13.

Shugaban Kula da Shirya Wasannin na Commonwealth David Gruvemberg ya sanar da cewa, ‘yan wasa 5 da suka fito daga kasashen Kamaru, Saliyo, Uganda da Ruwanda sun bata.

Gruvemberg ya shaida wa manema labarai cewa, sun fara gudanar da bincike kan lamarin.

Shugaban ya ce, a ranar 15 ga watan Mayu ne Visar ‘yan wasan ta za kare.

A ranar Larabar da ta gabata Kamaru ta sanar da cewa, ‘yan wasanta 8 da suka je halartar gasar sun yi layar zana inda aka neme su aka rasa.Labarai masu alaka