An fara zagaye da kofin duniya inda ya isa garin Sochi na Rasha

An kai samfurin kofin da za a ba wa wanda ya yi nasara a gasar kwallon kafa ta duniya ta 2018 zuwa birnin Soci na Rasha, kasar da za a gudanar da gasar.

853466

An gudanar da bikin karbar kofin inda zai kasance a garin har nan da ranar 26 ga watan Nuwamban 2017. Daga nan kofin zai ci gaba da zaga duniya na tsawon kwanaki 123 inda zai dawo Rasha a watan mayun shekara mai zuwa.

Za a gudanar da gasar ta FIFA 2018 a biranen Rasha 11 a tsakanin 14 ga Yuni da 15 ga Yulin 2018.Labarai masu alaka