An kashe wani dan wasan NBA a Amurka

An harbe Bryce Dejean- Jones dan wasan kwallon kwando NBA a gundumar Dallas ta Amurka

499729
An kashe wani dan wasan NBA a Amurka

An harbe Bryce Dejean- Jones dan wasan kwallon kwando NBA  a gundumar Dallas ta Amurka . Rahotanni da aka fitar na nuna cewa Bryce Dejean-jones dan wasan kwallon kwandon New Orleans Pelicans ya mutu sakamakon harbi da aka yi masa a Dallas aranar Asabar din nan. Rahotannin na nuna cewa makwabta sun ce  sun ji harbin bindiga ne kafin su fito ya fadi a bakin kofansa ya kasa motsi.

Dan wasa mai shekaru 23 ya rasa ransa ne yayin da aka isar da shi a asibiti inda a halin yanzu aka fara bincike na musamman don gano maharan.

A cikin wani hira da aka yi da manajar gidajen apartment da Bryce ke ciki, ya ce Bryce din ya yi kuskure ne ya farwa dakin wani bako maimakon shiga dakin abokinsa.

ReutersLabarai masu alaka