Tsohon dan wasa Micheal Jordan ya karya bajinta a duniya

Micheal Jordan ne ya samu kudin ritaya fiye da kowane dan wasa a duniya a shekarar 2015

463413
Tsohon dan wasa Micheal Jordan ya karya bajinta a duniya

Gwarzon wasan kwallon kwando na Amurka Micheal Jordan ne ya zama dan wasa da kudin ritayansa ya fi na kowane a shekarar 2015. Kamfanin mujallar Forbes ne ya fitar da sanarwar a ranar Alhamis din nan inda dan wasa Jordan ya karya bajinta a duniya. Rahoton na nuna cewa Micheal Jordan ya samu kudin ritaya Dala miliyan 110 a shekarar 2015.

Ga rahoton kuma ne aka yi jerin masu arziki a duniya inda Micheal Jordan ya zo na 1,741 a duniya. David Beckham, dan wasan kwallon kafa na Ingila wanda ya yi ritaya a shekarar 2014 ne ya zo na biyu a cikin jerin 'yan wasa da suka samu babbar kudin ritaya.

Jordan ya yi ritaya tun shekarar 2003 daga wasan NBA inda ya kafa kungiyar tasa kwallon Kwando Charlotte Hornets.Labarai masu alaka