Amfani da miyagun kwayoyi a wasannin motsa jiki kai tsaye

An zargi Shugaban hukumar IAAF na wasan motsa jiki kai tsaye Lamine Diack da cin hanci da rashawa.

427073
Amfani da miyagun kwayoyi a wasannin motsa jiki kai tsaye

Hukumar mai zaman kanta ta yaki da amfani da miyagun magunguna WADA ta ce an an samu shugaban IAAF da laifin cin hanci tun watan Nuwambar shekarar da ta gabata inda aka gudanar da bincike aka kori wasu yan wasan kasar Rasha inda ministan kula da harkokin wasanni na kasasr Rasha Vitaly Mutko ya yi watsi da zancen.
Sakamakon laifin ne Sebastian Coe ne ya maye gurbin Diack saboda binciken da aka fara na cin hanci da Diack ya yi inda ofishin yan sandan Faransa suka gudanar. An tsinti Daick din da kulla sharri gurin cin hanci da rashawa. An soki hukumar IAAF da rashin yaki da cin hanci da rashawa, rashin daidaitu da kuma rashin kyakkyawan shugabanci.

A shekarar 2013 ne aka gudanar da wasan motsa jiki kai tsaye a Moscow babban birnin kasar Rasha inda aka kama wasu masu wasanni 9 da amfani da miyagun magunguna don samun karfin gudu. A cikin shirye shiryen gudanar da wasan an ce shugaban kasar Rasha Putin ya bawa shugaban IAAF Diack kudi dala miliyan 25 maimakon miliyan 6 don samun damar watsa wasanni bisa talabijin a kasar.Labarai masu alaka