Abincin Turkiyya mai dadi da ya samo asali tun zamanin Daular Usmaniyya

Abincin Turkiyya mai dadi da ya samo asali tun zamanin Daular Usmaniyya.

A shirinmu na abinciccikan Daular Usmaniyya da muke kawo muku duk mako, a wannan satin za mu bayyana muku yadda ake hada “Shinkafar Kabuni”. Ana hada wannan shinkafa da Soffran, daya daga cikin kayan kamshi mafiya tsada a duniya. Shirin zai zo muku daga wajen kallo duniya na gilashi dake garin Tokat na Turkiyya.

Domin hada wannan abinci mai dadi ga kayayyakin da ake bukata:

naman rago kram 250

zallar mai cokali

shinkafa kofi 2

ruwa kofi 2.5

gyadar almong gram 50

bararriyar gyada cokali 1

cokali 2 na busasshen inibi

damki 1 na Soffran

Gishiri, cinnamon

Mai dafa abinci kuma mai binciken al’adu Yunus Emre Akkor ne yake mana bayanin yadda ake sarrafa wannan abinci mai dadi. Za mu zanga yankin Safranbolu tare. A sha kallo lafiya.