Turkiyya ta gwada wani jirgin ruwan yaki cikin nasara

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da cewa, jirgin ruwa na makami mai linzami na Atmaca ya yi nasarar harba makami inda ake bukata a gwajin da aka gudanar na karshe

1661142
Turkiyya ta gwada wani jirgin ruwan yaki cikin nasara

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sanar da cewa, jirgin ruwa na makami mai linzami na Atmaca ya yi nasarar harba makami inda ake bukata a gwajin da aka gudanar na karshe.

Erdogan, a cikin wata sanarwa a kan Twitter ya kara da cewa,

"Takobin bakin karfe na Blue Homeland  Atmaca Anti-Ship Missile ya sami damar harba makami inda ake bukata a karon farko a gwajin karshe da aka gudanar.. Sa'a ga Sojojinmu na kasa da na ruwa"

Shugaba Erdogan ya kuma raba hoton da aka dauka kafin harbe-harben gwajin makamin.Labarai masu alaka