An kubutar da masu neman mafaka 30 a tekun Turkiyya

An kubutar da masu neman mafaka 30 a gabar tekun gundumar Ayvalik din lardin Balikesir na Turkiyya bayan da jami'an tsaron tekun Girka suka kora su iyakar Turkiyya.

1634960

Jami'an tsaron tekun Turkiyya ne suka kai dauki yankin bayan samun labarin ganin masu neman mafaka a cikin jirgin ruwan roba.

An fito da masu neman mafakar zuwa gaba inda aka gano cewa, jami'an tsaron tekun Girka sun yi kora su iyakar teku ta Turkiyya.

An mika masu neman mafakar ga Cibiyar Mayar da 'Yan Gudun Hijira ta gundumar Ayvalik.

 Labarai masu alaka